Shekara biyar: Shin ina labarin ‘yan Matan Chibok?

Iyayen 'yan matan Chibok sun ce suna cikin tashin hankali tsawon shekara biyar
Hakkin mallakar hoto
Reuter
Image caption

Shekara biyar kenan da sace ‘yan matan sakandare 276 a garin Chibok, arewa maso gabashin Nijeriya.

An sace dalibai ‘yan matan ne ranar 14 ga watan Afrilun 2014, lamarin da ya dimauta al’ummar duniya, tare da janyo gangami da kiraye-kirayen lallai a ceto su.

Iyayen ‘yan matan sun ce tsawon shekaru biyar suna cikin tashin hankali, ko da yake sun ce har yanzu ba su cire tsammani ba, kamar yadda mahaifiyar daya daga cikin ‘yan matan ta shaidawa BBC.

An yi nasarar kubutar da wasu daga cikinsu, amma akwai sauran ‘yan mata 112, wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

A wata sanarwa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai huta ba har sai ya sake hada ‘yan matan da iyayensu.

Shin suna raye?

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images
Image caption

Ana tunanin wasunsu daga cikin ‘yan matan sun yi aure har da ‘ya’yansu

Babu tabbaci kan ko ‘yan matan da suka rage a hannun Boko Haram suna raye ko wani bayani kan inda ake garkuwa da su.

Wasu rahotanni sun ce an ga wasunsu a Kamaru, amma babu wata majiyar gwamnati da ta tabbatar da wannan

Amma akwai alamomin da suka nuna cewa yawancinsu sun yi aure har da ‘ya’ya.

Abubuwan da suka faru

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Makarantar sakandaren Chibok da aka sace ‘yan matan

Mayakan Boko Haram sun yi wa sakandaren ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno tsinke a ranar 14 ga Afrilun 2014, suka kwashe dalibai 276.

Lokaci ne da ya shiga babin munanan abubuwan tarihi da jefa duniya cikin firgici da kaduwa.

Mako biyu bayan sace su ne, wasu mata suka fara gangami ta hanyar zanga-zanga, abin da ya zama mafari ga fafutukar neman a ceto ‘yan matan Chibok mai taken #BringBackOurGirls.

A ranar 5 ga watan Mayu kuma, Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani faifan bidiyo ya fito ya amsa cewa su ne suka sace ‘yan matan Chibok.

Kwamitin gano gaskiya da Burgediya Janar Ibrahim Sabo ya jagoranta ya ba da rahoto ranar 21 ga watan Yunin 2014, inda ya ce babu dalibar da aka ceto bayan 57 da suka kubuta tun farko.

Satar ‘yan matan Chibok ta yi matukar jan hankalin al’ummar duniya, inda a ranar 14 ga watan Yuli fitacciyar matashiyar nan mai rajin bunkasa ilmin mata a duniya, Malala Yusoufzai ta ziyarci Najeriya.

Masharhanta da dama na ganin cewa al’amarin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan wanda aka kayar a zaben 2015.

Jim kadan da rantsar da shi kan mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin karya kashin bayan Boko Haram tare da alkawalin ceto ‘yan matan Chibok.

Sai dai kimanin wata shida bayan wannan alkawari a ranar 14 ga watan Janairun 2016, Daruruwan iyayen ‘yan matan Chibok suka yi wani maci a Abuja domin nuna juyayi bayan cika kwana 600 da sace ‘yan matan Chibok.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ranar 19 ga watan Mayun 2016, rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa game da Amina Ali ‘yar sakandaren Chibok ta farko da aka gano a yankin Damboa. An gan ta ne dauke da jariri.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuma a ranar 22 ga Satumba, ya gayyaci Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani don tattaunawa da Boko Haram ta yadda za a yi musayar ‘yan matan Chibok.

Ba da dadewa ba kuma sai wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ya shaida wa BBC ranar 13 ga watan Oktoba cewa an saki ‘yan matan Chibok 21.

Bayan wata bakwai, a ranar 7 ga watan Mayun 2017 fadar shugaban Najeriya ta ce ‘yan matan Chibok 82 da Boko Haram ta sako a ranar Asabar biyu ga wata, sun isa Abuja.

A ranar 14 ga Janairun bara, Dan jaridar nan mai ba da rahotanni kan kungiyar Boko Haram a Najeriya Ahmed Salkida, ya ce ‘yan matan Chibok 15 kawai suka rage a raye cikin 112 da har yanzu ke hannun kungiyar.

Gwamnatin kasar dai ta yi watsi da wannan labari, inda ta ce har zuwa lokacin suna ci gaba da tattaunawa don ganin an saki ragowar ‘yan matan.

Kwanaki bayan nan Boko Haram ta fitar da wani bidiyo dauke da wasu daga cikin ragowar ‘yan matan Chibok. Bidiyon ya nuna daya daga cikin matan sanye da shudin hijabi da farin nikabi tare da wasu mata kimanin goma.

Kamar ba a dauki darasi kan sace ‘yan matan Chibok ba, a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, Boko Haram ta kuma sace ‘yan matan sakandare 110 a makarantarsu da ke Dapchi a jihar Yobe. Al’amarin ya sake jefa Nijeriya cikin rudani da tunanin ‘yan matan Chibok.

Baya ga rukunin ‘yan matan Chibok da aka kubutar, an kuma gano daidaikunsu a lokuta daban-daban. Salomi Pagu ita ce ta baya-bayan nan da aka gano ranar 5 ga watan Janairun 2018.

Boko Haram a takaice

Hakkin mallakar hoto
AFP
  • A 2002 aka kirkiri Boko Haram da ke wa’azi kan kyamar ilimin boko
  • Ta kaddamar da yaki ne a 2009, inda ta kwace ikon garuruwa tare da kafa daula
  • Dubban mutane aka kashe, an sace daruruwa da suka kunshi har da ‘yan mata dalibai, kuma an raba miliyoya da gidajensu
  • Ta kulla alaka da kungiyar IS a 2015, tare da kiran kanta kungiyar IS a yammacin Afirka
  • Boko Haram ta rabu gida biyu bayan sabani tsakanin shugabanninta a 2016
  • Sojoji sun kwato garuruwa da dama a shekaru hudu da suka gabata, amma har yanzu Boko Haram barazana ce

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...