Sheikh Giro ya nemi afuwar ‘yan Najeriya game da tsine wa “makiyan” Buhari

Malamin Izala a Najeriya, Shiek Abubakar Giro Argungu, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya a kan wani bidiyo da yake nuna malamin yana kakkausan kalamai a kan “makiya” Shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Malamin ya bayyana cewa bidiyon an nade shi ne tun a 2015 kuma ya yi kalaman ne sakamakon wata matsala da ta faru a siyasar wancan lokaci.

Bidiyon dai ya nuna Malamin yana kwashewa marasa goyon bayan Buhari albarka sa’annan ya yi wa marasa ci gaban Najeriya fatan hatsarin mota.

Sheik Abubakar ya ce ya yi nadamar yin wadannan kalamai kuma ya amince da kuskurensa.

Malamin ya ce a wancan lokaci ya yi raddi ne ga wata kabila mai suna ‘yan tatsine.

Tun bayan da guguwar siyasar 2019 ta fara kadawa a Najeriyar aka samu rarrabuwar kai na malamai musamman na Izala a kasar.

A kwanakin baya an samu sabanin ra’ayi da Sheik Ahmed Gumi wanda daya daga cikin Malaman Izala ne a kasar.

Haka a wani bangaren an samu sabanin ra’ayi da Shiek Yusuf Sambo Rigachikun bayan ya bayyana ra’ayinsa na goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...