Connect with us

Hausa

Shehu Sani na son matar El-Rufai ta daina magana akan gashinsa

Shehu Sani, sanata dake wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya nemi gwamna Nasiru el-Rufa’i da jawa matarsa kunne kan yadda take yawan magana akan gashin kansa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook sanatan ya ce matar gwamnan, Hadiza el-Rufai ko da yaushe tana magana akan gashin kansa a duk lokacin da ta fita yakin neman zabe.

Hadiza wacce mawallafiyar littafai ce ta kasance akan gaba-gaba wajen yakin neman zaben mijinta gabanin zaben gwamnan da za a gudanar ranar cikin watan Maris.

“Ina rokon Gwamna da ya gargadi matarsa da ta daina magana akan gashina a duk sa’ilin da taje yakin neman zabe.Duk inda taje maganar bata wuce ta gashina.Ba laifina bane idan mijinta bashi da arzikin gashi.Na dauki abin da take a matsayin kalaman batanci,zan kai kararta wurin Sheikh Gummi ko kuma majalisar Limamai. Haba jama’a,” a cewar sakon.

Wannan ne dai karo na farko da sanatan yayi musayan yawu da matar gwamnan.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mai shari’a Walter Onnoghen ya daukaka kara

Justice Walter Onnoghen

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan shi ne karon farko da aka gurfanar da Alkalin Alkalai a Najeriya a gaban kotu aka kuma yanke masa hukunci

Tsohon Babban Mai shari’a na Najeriya na baya bayan nan Justice Walter Onnoghen ya daukaka kara a kan hukuncin da kotun da’ar ma’aikata ta yanke masa kan laifin kin bayyana biyar daga cikin asusun bankunansa wadanda ke dauke da tarin kudaden waje.

Onnoghen ya gabatar da korafe-korafe guda 16 a gaban kotun daukaka karar a Abuja, jim kadan bayan da kotun da’ar ma’aikatan ta yanke masa hukunci ranar Alhamis.

A daya daga cikin korafe-korafen da ya gabatar ya kafe cewa bai taba amsa laifin cewa ya aikata laifukan da kotun ta zarge shi da su ba, kamar yadda kotun da’ar ma’aikatan ta ce.

Takardar daukaka karar ta kara da cewa, ”Mai daukaka karar (onnoghen) bai amsa laifin kin bayyana dukiyarsa ba daga shekara ta 2005 a matsayinsa na mai shari’a na kotun koli.

”Mai daukaka karar kawai ya bayyana cewa bai bayyana ba ne a shekara ta 2009 kamar yadda aka bukata, saboda ya manta, kuma nan da nan ya bayyana bayan da ya gano hakan.”

Justice Onnoghen ya kuma ce kotun da’ar ma’aikatan ta yi kuskure a tsarin shari’a, kan korar korafin da ya shigar na kalubalantar ikonta na yi masa shari’a, wanda hakan ya keta haddin shari’a.

Haka kuma ya ce kotun ta yi kuskure a tsarin shari’a, kan korar bukatarsa da ta yi wadda a ciki ya nemi alkalin kotun da ya dakatar da yi masa sharia’a bisa zargin nuna bambanci ko san zuciya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Lauyoyi masu kare Justice Walter Onnoghen a yayin wani zama na kotun da’ar ma’aikata

A takardar daukaka karar, Justice Onnoghen ya gabatar da bukatar kotun daukaka karar ta bayar da damar sauraran karar da ya daukaka, sanna kuma ta yanke hukuncin cewa kotun da’ar ma’aikatan ba ta da hurumin sauraren wannan shari’a tasa.

Bugu da kari ya bukaci kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin da waccan kotun ta yi masa, kana ta wanke shi kuma ta sallame shi, baya ga wasu bukatun kuma.

Ita dai kotun da’ar ma’aikatan ta samu Mai shari’a Onnoghen da laifi, ta kuma cire shi daga mukamin babban mai shari’a na Najeriya, da kuma mukamin shugaban hukumar da’ar ma’aikata(CCB).

Haka kuma ta haramta masa rike wani mukami na gwamnati a tsawon shekara 10, baya ga umartarsa da ya mika dukkanin asusun banki biyar wadanda bai bayyana mallakarsu ba a tsakanin 2009 da 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu sun yi zargin cewa shari’ar ta Onnoghen tana da alaka da siyasa, saboda an fara ta ne gab da babban zaben kasar

Dakatar da Onnoghen a can baya ya jawo ce-ce-ku-ce da dama a Najeriya, inda har kungiyar lauyoyin kasar ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen.

Kungiyar ta bukaci mambobinta da su kaurace wa kotu har na tsawon kwana biyu, umarnin da wasu suka bi wasu kuma suka yi burus da shi.

Haka kuma a lokacin dakatarwar, babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Tarayyar Turai sun yi Allah-wadai da dakatar da shi.

Shugaba Buhari dai ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da’ar ma’aikata wacce ta same shi da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi mukamin alkalin alkalan a shekarar 2017.

An zargi Shugaba Buhari da katsa-landan a harkokin shari’a saboda gurfanar da Onnoghen a kotun, ko da za a kalubalanci sakamakon zabensa a kotun koli, inda ake ganin Onnoghen a matsayin barazana ga nasarar ta Buhari idan yana kan matsayinsa na Babban Mai shari’a na kasar.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

N30,000 Ya Zama Mafi Karancin Albashin Ma’aikata a Najeriya

Shi dai wannan kuduri da yanzu ya zama doka, zai nuna a sabon tsarin biyan ma’aikatan Najeriya albashinsu.

Tun farko dai Majalisa ta amince da dokar biyan mafi karancin albashi na N30,000.

Wasu gwamnonin jihohi dai sun nuna rashin amincewarsu da wannan doka, suna mai cewa ba zasu iya biyan ma’aikatansu mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwar dake cewa shugaba Buhari ya sanya hannu a sabuwar dokar mafi karancin albashi. Daga yanzu N30,000 ne mafi karancin albashi.

Bayan dogon lokaci da kungiyoyin kwadago suka dauka suna neman Majalisun Najeriya su amince da kudirin dokar mafi karanci albashi ta N30,000 yanzu haka fadar shugaban kasa dsa ‘yan Majalisun sun amince.

Majalisar Dattawan Najeriya ta bi sahun takwararta ta Wakilai wajen amincewa da kudirin dokar Naira dubu talatin a matsayin albashi mafi karanci da za a biya ma’aikaci, bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana gwagwarmaya da kungiyoyin kwadago.

Facebook Comments
Continue Reading

Crime

‘Yan bindiga sun kai hari a jihar Jigawa

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta tabbatar cewa barayi sun halaka mutum daya tare da jikkata wasu mutane, a wani hari da barayin suka kai a garin Maidawa da ke jihar.

Bayanai sun ce maharan sun shiga kauyen ne kan babura, sannan suka je gidan wani attajiri a kauyen suka karbi kudi, suka kuma harbe shi tare da wasu mutanen garin.

Cikin wandanda aka harba har da wasu yara uku kamar yadda aka bayyana.

Duk da cewa ‘yan sanda sun bayyana cewa mutum daya aka kashe, amma mazauna garin na ikirarin kashe mutane da dama a harin da barayin suka kai.

An bayyana cewa barayin sun kai kusan mintuna arba’in suna cin karensu ba babbaka a cikin garin na Maidawa.

Mazauna kauyen sun koka bisa ga faruwar wannan lamarin inda suke ganin kamar irin abubuwan da ke faruwa a wasu wurare sun fara isowa yankin su.

Wasu kuma mazauna garin sun shaida cewa da wayansu ba su taba ganin an kawo hari da bindigogi ba a garin.

Wannan harin da aka kai a Jigawa na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ke kara kamari musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Sai dai gwamnatin kasar ta bayyana cewa tana iya bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: