SHARHI: Yunkurin Shugaba Buhari Na Sasanta Rikicin Siyasa A Jihar Kaduna Abin A Yaba Ne – El-Bash

[ad_1]

Hakika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abin a yaba masa akan yunkurin sasanta rikicin siyasar jihar Kaduna, tsakanin Malam Nasiru El-rufai da Sanata Shehu Sani, wanda yin hakan babbar nasara ce ga jam’iyyar APC .

Duk da cewa hakan ba zai yi wa wasu dadi ba, musamman jam’iyyar adawa ta PDP, da kuma wadanda suka mayar da rikicin hanyar neman gindin zama da samun kudi. Amma babbar nasara ce ga shi kansa gwamnan jihar Malam Nasiru El-rufai da ma jam’iyyar APC.

Ga duk wanda yake bibiyar siyasar jihar Kaduna, zai ga cewar mafi yawan masu hada irin wannan fitina ba ‘yan asalin jam’iyyar APC bane kuma suna yin hakan ne domin amfanin kansu ba wai don cigaban jihar ba.

Malam Nasiru El-rufai mutum ne mai hankali, hikima da hangen nesa, kuma na san kai kanka za ka yi matukar farin ciki idan aka wayi gari aka ce an samu sasanci tsakanin ka da Sanata Shehu Sani. Ka yi amfani da ilimin ka wajen yin watsi da wadanda suke yi maka bambadanci domin amfanin kansu.

Daga bayyanar wani hoto da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daga hannun Sanata Shehu Sani, mun ga mafiya yawan masu hada irin wannan fitina a jihar Kaduna suna zage-zage, saboda abin bai yi masu dadi ba, yayin da mafiya yawan ‘yan jam’iyyar APC abin ya yi masu dadi. Cikin wadanda suka yi farin ciki har da manyan jami’an gwamnatin Baba Buhari.

Muna fatan za’a samu hadin kai tsakanin manyan jagororin guda biyu. Kuma muna fatan shugaban kasa muhammadu Buhari zaici gaba da shiga tsakani.

Fatan mu 2019 Malam Nasiru El-rufai ya koma Gwamna. Shehu Sani ya koma Sanata, matukar suna jam’iyyar APC.

[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...