Sergio Ramos ya buga El-Clasico sau 40

Sergio Ramos

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sergio Ramos, kyaftin din Real Madrid, ya zuwa yanzu ya buga wasa 40 a karawar hamayya da ake kira El-Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid.

Ramos ya yi karawa ta 40 a ranar Laraba a fafatawar da kungiyoyin biyu suka tashi 1-1 a Copa del Rey wasan zagayen farko na daf da karshe da suka yi a Camp Nou.

Kawo yanzu kyaftin din na Real Madrid ya haura Lionel Messi na Barcelona wanda ya yi wasa 30 a karawar ta El-Clasico.

‘Yan wasa uku ne kawo yanzu ke kan gaba wajen buga El-Clasico da yawa da suka hada da Paco Gento da Sanchís daga Madrid da Xavi na Barcelona da kowanne ya yi fafatawa 42.

Ramos wanda ya buga El Clasico 40 ya ci kwallo hudu, inda biyu a Santiago Bernabeu da wasu biyun a Barcelona.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne Barcelona za ta ziyarci Santiago Bernabeu a wasa na biyu na daf da karshe a Copa Del Rey.

Barcelona ta lashe Copa del Rey 30, ita kuwa Real Madrid tana da shi 19.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...