‘Sau 200 Shehu Shagari yana sauke Qur’ani tun hambarar da gwamnatinsa’

Tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari

Hakkin mallakar hoto
Family

Jikan tsohon shugaban Najeriya marigayi Alhaji Shehu Shagari ya rubuta wa kakansa wasika mai sosa rai bayan rasuwarsa.

Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Juma’a 28 ga watan Disamban 2018 a Abuja yana da shekaru 93.

A cikin wasikar da babban jikansa Bello Bala Shagari, shugaban majalisar matasan Najeriya (NYCN) ya rubuta kuma ya aika wa BBC, ya tabo batutuwa da dama da suka faru bayan rasuwar Kakansa tun da daga Jana’iza har zuwa ta’aziyarsa da kuma batutuwan da suka shafi siyasa da wasu halayen marigayin.

Ya rubuta wasikar ne ta musamman zuwa ga Kakansa marigayi Shagari kan abubuwan da suka faru bayan rasuwarsa.

A cikin wasikar ya shaida wa kakansa cewa rasuwarsa ta zo ne a daidai lokacin siyasa a Najeriya.

Ya ce akwai takarda da marigayi Shagari yake rubuta adadin yawan saukar Al Qur’ani mai tsarki da ya yi.

“Mallam da fatan kana hutawa lafiya? Nakan yi mamakin ribar ayyukanka bayan ka yi saukar Al Qur’ani fiye da 200 a cikin shekaru 34 bayan ritaya.” in ji shi.

Ya kuma tabo batun ce-ce-ku-ce da aka dinga yi kan zuwan shugaba Buhari ta’aziyar marigayi Shagari inda har wani bangare daga cikin iyalansa suka nuna bacin ransu kan abin da Buhari ya rubuta a kundin rijistar ta’aziyar marigayin.

Sai dai a cikin wasikar bai fadi abin da shugaba Buhari ya rubuta a kundin rijistar da har ya fusata iyalan Shagari ba.

Sai dai ya kare shugaban inda ya ce ya karrama Kakansa tun da har ya bayar da umurnin a sassauta tutar Najeriya tare da alkawalin kafa cibiya domin tunawa da tsohon shugaban na Najeriya.

Amma a cikin wasikar, ya sanar da marigayin cewa babban amininsa Janar Yakubu Gowon har yanzu bai zo yin ta’aziya ba, da kuma wanda ya kira dansa Adamu Mu’azu.

Amma ya ce tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya zubar da hawaye a lokacin da ya zo ta’aziya, sannan tsohon shugaban soja Janar Badamasi Babangida ya ta kira ta waya ba sau daya ba saboda yana kasar wajen lokacin rasuwar.

Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Me Buhari ya rubuta a kundin rijistar rasuwar Shagari?

Ya yi gugar-zana kan yaki da rashawa da gwamnati mai ci ke ikirarin tana yaki akai, inda ya ce duk da an dauki gwamnatin kakansa a matsayin wadda cin hanci da rashawa ya fi yi wa katutu a tarihin Najeriya amma babu wanda zai nuna yatsa ga Shagari.

Ya ce kakansa ya koya ma sa fadin gaskiya komi dacinta. “Nakan yi dariya idan na ji wasu suna magana kan mutum mai gaskiya da aminci.”

“Nakan tambaye su mene ne ma’anar mutum mai gaskiya”? ai shi ne ministan kudi na shekara shida amma ba ya da halin da zai dawo da iyalansa gida nan take bayan ya bar ofis.”

“Mai gaskiya shi ne ka yi minista sau bakwai amma ka yi ritaya kuma ka dawo ka nemi kansila a karamar hukuma.”

“Mai gaskiya shi ne wanda ya taba zama shugaban kasar Najeriya mai arzikin fetir kuma ya yi ritaya amma a cikin asusun ajiyarsa na banki bai mallaki kasa da N67,000, kuma babu inda ya saka jari a ciki da wajen Najeriya ba,” in ji Bello Shagari.

Ya kuma ce Shagari wanda shi ne tushen Abuja amma ba ya da gida a Abuja balle fili, har sai da Obasanjo ya ba shi gida a unguwar Maitama.

A cikin wasikar ya ce akwai bayanai da dama game da marigayi Shagari inda nan gaba zai bayyana wa duniya.

Wane ne Shehu Shagari?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

  • Dan asalin jihar Sakkwato ne a arewa maso yammacin Najeriya
  • An haife shi a shekarar 1925 a garin Shagari
  • Shi ne na shida ga maifinsa Aliyu
  • Dan siyasa ne Manomi kuma makiyayi
  • Malamin Makaranta ne marubucin wakoki da tarihi
  • Ya zama shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar NPN
  • Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983
  • Bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a mulkin soja
  • Kafin Shagari ya zama shugaban kasa ya taba zama sakataren majalisar Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa
  • Ya rike mukaman minista daban-daban
  • Ya taba zama ministan ci gaban tattalin arziki a shekarar 1960
  • Ya taba zama ministan kula da harkokin cikin gida a shekarar I962
  • Ya taba rike ministan ayyuka da safiyo (1965).
  • Shagari ne Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.
  • Ya rasu ne a ranar juma’a 28 ga watan Disamban 2018

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...