Sarkin Musulmi Ya Buƙaci Musulmi  Su Fara Duban Watan Shawwal Ranar Litinin

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya nemi Musulmi da su fara duban watan Shawwal tun daga ranar Litinin.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Sambo Wali shugaban kwamitin bada shawara na masarautar Sokoto kan harkokin addini ya ce duk wanda ya ga watan to yayi ƙoƙari ya sanar da hukumomin da suka dace.

“Saboda haka ana buƙatar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Shawwal na 1445 AH tun daga ranar Litinin su kuma kai rahoton haka ga ofishin hakimi ko dagaci mafi kusa domin a gabatarwa Mai Alfarma, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar Sultan na Sokoto,” a cewar sanarwar.

Idan aka ga watan ranar Litinin to hakan ya kawo ƙarshen watan Azumin Ramadana.

More from this stream

Recomended