Ronaldo na dab da lashe kofi bayan barin Santiago

Ronaldo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ronaldo ya bar Real Madrid a karshen kakar bara bayan da ya lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Juventus ta samu nasarar doke AC Milan a wasan hamayya da suka fafata a filin wasa na Allianz Stadium da ke birnin Turin.

Wannan sakamako na nufin cewa idan Napoli ta yi rashin nasara a hannun Genoa a ranar Lahadi, kenan Juventus ta dauki kofin na bana, wanda kuma shi ne na takwas a jere.

AC Milan ce ta fara zura kwallo a wasan, inda dan wasanta Krzyszt ya daga ragar Juve kafin zuwa hutun rabin lokaci, to amma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci Paulo Dybala ya farke kwallon da bugun fenareti.

Sai dai kuma ana saura minti shida a tashi daga wasan Kean, wanda magoya bayan kungiyar suka nuna wa wariyar launin fata a wasan da suka yi ranar Laraba da kungiyar Cagliari ranar Laraba, ya zura kwallon da ta bai wa Juventus nasara a wasan.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...