Connect with us

Hausa

Real Madrid ta sayo Eder Militao

FC Porto

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar Real Madrid, ta dauki mai tsaron baya na kulob din FC Porto, Eder Militao.

Dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da Zinedine Zidane ya saya, bayan da ya sake karbar aikin kocin Madrid.

A sanarwar da Real ta sanar a shafinta na Intanet ta ce ”Real Madrid ta cimma yarjejeniya daukar dan wasan FC Porto, Eder Militao”.

Dan kwallon na Brazil ya amince zai koma Spaniya kan shekara shida, zai kuma koma can ne idan an kammala wasannin bana.

Rahotanni na cewa kudin daukar dan kwallon Brazil din ya kai fam miliyan 43.5, ana sa ran yarjejeniyarsa da Real za ta kare a karshen watan Yunin 2025.

Militao ya fara buga tamaula a Sao Paulo daga nan ya koma FC Porto a watan Agustan 2018, ya kuma taimakawa kungiyar Portugal ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta bana.

Tuni aka fitar da Real Madrid a gasar kofin Zakarun Turai da kuma Copa del Rey, sannan tana ta uku a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona ta daya.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jinsin jakai na barazanar karewa a duniya | BBC Hausa

Jakuna uku

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fasa-kwauri da cinikin fatun jakai, abu ne da ke ci gaba da jan hankalan masu ruwa da tsaki da mahukunta a fadin duniya.

Sun ce yanka dabbobin ba ya rasa nasaba da gagarumin neman da ake masu a kasar China wajen hada magungunan gargajiya.

A makon jiya ne majalisar dokokin Nijeriya ta yi zaman jin ra’ayoyin jama’a kan wani kudurin doka na Honarabul Garba Datti Muhammad da ke neman haramta yanka da fataucin jakai zuwa ketare.

Cikin mahalarta zaman, har da jami’an wata gidauniya ceto jakai mai fafutuka don inganta rayuwar jakan da alfadarai da ma mutane ta Burtaniya.

Simon Pope, babban jami’i a gidauniyar Donkey Sanctuary ta kasar Birtaniya ya ce abin bakin ciki ne idan aka yi la’akari da amfanin jaki a rayuwar dan adam a matsayin wani abun sufuri kamar mota.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mista Pope ya kuma ce mafi yawan fatun da ake safara suna fitowa ne daga Afirka.

Ya ce “Najeriya musamman na jan hankalin masu sayen fatar jakai saboda yawansu a nan.”

Ya kuma ce a kalla akwai jakai miliyan daya da dubu dari uku a kasar.

“Sai dai wani dan kasuwa ya bayyana cewa ana yanka a kalla jakai dubu biyu da dari biyar a kasuwarsu kullum”, in ji Mista Pope.

Hakan kuma ya nuna ana kashe jakai kusan dubu dari shida duk shekara.

Ya ce duk da cewa jakan Najeriya na da yawa, amma da wannan adadin da ake yankawa za a wayi gari babu jaki ko daya a kasar.

Mista Pope ya ce rayuwar jakuna na da muhimmanci matuka saboda irin gudumawar da suke bayarwa wajen taya aikace-aikace musamman ma a Najeriya.

Da yawa daga cikin mutanen karkara a Najeriyar dai sun ta’allaka kan jaki a matsayin abin hawa zuwa kasuwa da zuwa gonaki har da kai iyalai asibiti a lokutan haihuwa.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Gwamnati ta yi sakaci kan matsalar tsaro a Najeriya- PDP

tutar jam'iyyar PDP

Hakkin mallakar hoto
BUZZ NIGERIA

Babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce matsalolin da al’ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya sa rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki.

Sanata Umaru Tsauri, sakataran kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC.

Ya ce rashin fadar gaskiyar lamurra game da halin da kasa ke ciki daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka jefa kasar cikin halin rashin tsaron da take ciki.

Ya ce “babu abin da ya jawo wannan matsala illa gwamnati ta ki yarda ta fadi wa mutane gaskiya cewa wannan abu na faruwa, kuma a dauki mataki.”

Ya kuma ce aikin gwamnati ne ta gano wadanda ke da hannu cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar tsaro a Najeriya, ba jama’ar kasar ba.

Sanata Umaru Tsauri ya ce halin da Najeriya ta shiga ba ya yi wa su kansu ‘yan adawa dadi saboda lamari ne da ya shafi kowa a kasar.

“Mu ‘yan adawa abin da muke so shi ne a gamsu, a yarda cewa abubuwan da ke faruwa sun shafi mutane, kuma mutanen nan lallai ne a yi abinda aka tsayar da abin da ke faruwa gare su,” a cewarsa.

Ya ce abin yi yanzu shi ne gwamnati ta binciko tushen matsalar, sannan ta yarda cewa matsalar ta fito fili sannan ta nemi maganinta ta hanyar amfani da dimbin mutanen da ke cikin gwamnati.

“A kullum gwamnati na nuna cewa tashin hankalin bai kai yadda ake tsamanninsa ba, don kuwa a kullum wadanda ake garkuwa da su talakawa ne.” in ji Sanata Tsauri.

Ya ce idan aka sace wani babba a gwamnati ba a sakin jiki, don haka me zai hana ba za a dauki irin wannan matakin ba a kodayaushe?

Matsalar tsaro, musamman ta garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a arewacin Najeriya ta zama daya daga cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu kuma kalubale ga gwamnati mai ci.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Yan Bindiga Sun Zafafa Kai Farmaki A Wasu Yankuna

Bayan da yan bindiga dadi da masu satar mutane suka dai-dai ta da dama daga cikin yankunan jihar Zamfara, wannan ta’addancin dai halin yanzu na neman samun gindin zama a jihar Katsina.

A cikin kanan hukumoni tara dake dandana kudarsu, karamar hukumar Batsari itace kan gaba inda yau kwanaki shidda ke nan jere ‘yan bingigan suke tada gari.

Malam Sani Lawal wani mazaunin Karamar hukumar da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hare hare a kauyuka da dama inda suka yi kone kone suka kuma janyo asarar rayuka da kaddarori. yace sun je Kasai da Wagini suka kashe mutune sannan suka kore masu dabbobi. Bisa ga cewarshi, ‘yan bindigar sun kuma tafi garin Yar’gamji suka kashe mutane goma sha ukku, wadanda aka kai gawarwakinsu kofar gidan sarkin Batsari.

Mallam Lawal ya bayyana cewa, wadansu mutanen an kashe su ne suna gonakinsu, yayinda yace ‘yan bindigar sun tada mutanen karamar hukumar Safana baki daya, sai dai Sashen Hausa bai sami tabbacin haka daga wata majiya ba. Mallam Sani Lawal dai ya bayyana fusata da bakin cikin ganin a cewarsa, gwamnati bata daukar matakin da ya kamata na shawo kan matsalar.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: