Rashin kayan aiki yana kawo wa yaƙi da rashin tsaro cikas a Abuja—Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a ranar Litinin ya bayyana cewa rashin isassun kayan aiki da motocin aiki na kawo cikas wajen yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja.

Wike, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma dora laifin yawaitar sace-sacen mutane a wasu al’ummomin da ke kan iyaka na babban birnin tarayya Abuja da rashin kayan aiki da za a yi amfani da su wajen gano masu aikata laifuka.

Sai dai ya tabbatar wa mazauna yankin cewa nan ba da dadewa ba za a magance matsalolin tsaro bayan amincewar da shugaba Bola Tinubu ya yi na sayo kayan aiki na gaggawa.

Ya ce an amince da sayo kayan aikin bin diddigi da motocin aiki don taimakawa wajen gano masu garkuwa da mutane.”

More from this stream

Recomended