Philippines: Ana gudanar da zaben raba gardama

Rodrigo Duterte

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte

A kalla mutum miliyan uku ne ake sa ran za su kada kuri’a a zaben raba gardama da za a yi a lardin kudancin Philippines a yau Litinin.

Ana dai tambayar masu zaben ne ko sun amince da a kirkiro wani yanki mai cin gashin kansa na Musulmi a yankin Mindanao.

Yankin na Bangsomoro zai zama wata sabuwar hanyar samar da zaman laifiya tsakanin Musulmi ‘yan aware da da sojojin gwamnatin kasar.

Fiye da mutum 120,000 sun rasa rayukansu kuma an tarwatsa kimanin mutum miliyan biyu daga muhallansu.

Dukkan gwamnatocin kasar Philippines sun shafe shekaru kusan 60 suna kokarin samar da tabbataccen yanayin zaman lafiya tare da kungiyar Moro Islamic Front, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Amma a yau akwai wata sabuwar dama cewa zaben raba gardama da za a yi, wanda kuma ake sa ran zai samar wa yankin ikon gudanar da harkokinsa zai iya zama mafitar da aka dade ana nema.

A nata bangaren, gwamnatin kasar na fatan mayakan a yankin za su ajiye makamansu, lamarin da ka iya kawo zaman lafiya a karon farko cikin shekaru masu yawa.

An dai sha samun rikice-rikice tsakanin mayakan da dakarun gwamnati a ‘yan shekarun baya, mafi shahara a cikinsu shi ne na Mama-sapano a shekarar 2015 inda a kalla mutum 60 suka rasa rayukansu.

Samar da zaman lafiya a yankin na daga cikin manyan alkawuran da Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya yi a lokacin da yake neman darewa karagar mulkin kasar.

Wannan zaben raba gardamar na cikin ayyukan da ya shirya domin cika alkawarin nasa.

Idan aka amince da sabon tsarin mulkin wannan yankin a wajen zaben raba gardamar, gwamnatin kasar za ta sami karfin gwuiwar kafa tsarin mulki na Tarayya a fadin kasar.

More News

Gobara ta kama wani sashe na kotun ƙolin Najeriya

An samu tashin gobara a wani sashe na Kotun Kolin Najeriya dake birnin tarayya Abuja. Kawo yanzu babu wani bayani kan musabbabin tashin gobarar amma...

Gobara ta kama wani sashe na kotun ƙolin Najeriya

An samu tashin gobara a wani sashe na Kotun Kolin Najeriya dake birnin tarayya Abuja. Kawo yanzu babu wani bayani kan musabbabin tashin gobarar amma...

Yan bindiga sun sace kwamishinan yaɗa labarai na Benue

Yan bindiga sun yi garkuwa da, Matthew Abo Kwamishinan Yada Labarai, Al'adu da Yawon Bude Ido na jihar Benue. An yi garkuwa da Abo a...

Nan bada jimawa za a kawo karshen rashin wutar lantarki a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta roki mazauna jihar da su kara hakuri inda ta ce rashin wutar lantarki da ake fuskanta a jihar zai zo...