Osinbajo Ya Sallami Shugaban Hukumar Tsaro Ta DSS

Sanarwar mukaddashin shugaban ta zo ne daidai lokacin da jami’an tsaro su ka dauki matakin hana wasu ‘yan majalisa shiga majalisar da hasashen barin wasu su shiga don yunkurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Duk da sanarwar ba ta danganta lamarin kwabe Lawal Daura da abun da ya faru a majalisa ba, memba a hukumar ‘yar sanda Naja’atu Muhammad ta ce matakin haka ya ke nufi kuma ya dace.

A cewarta, shi ya tura jami’an tsaro su ka mamaye majalisa don haka matakin kwabe shi da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ya yi daidai.

Ta ci gaba da cewa, majalisa ita ce ta bambanta mulkin soja da na dimokradiyya, don haka ‘yan majalisar ko da sun kasance dujal, su suke wakiltar mu.

Yanzu dai za a jira a ga yanda ‘yan majalisa masu hamayya da juna za su kammala wannan takaddama da ta ke kama da wasan kwaikwayo a yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na hutun kwanaki 10 a Landan.

Saurari cikakken rohoton

 

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...