Nijar ta samu tallafi maganin malaria daga Amurka

Sauro ne ke haddasa cutar malaria

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Amurka ta tallafa wa jamhuriyar Nijar da magungunan zazzabin cizon sauro wato malaria na milyoyin CFA.

Tallafin dai ya hada da magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro dama na magance cutar da zarar an kamu da ita.

Kazalika daga cikin tallafin da Amurkan ta ba wa Nijar, akwai gidajen sauro.

Amurka dai ta bayar da wannan taimako ne ga Nijar da zimmar rage yaduwar cutar ta malaria da akshi 50 cikin 100.

Wannan tallafi na Amurkan, na daga cikin wani tsari ne na kasar wajen tallafa wa kasashe masu tasowa.

Cutar zazzabin cizon sauro na daga cikin cututtukan da ke saurin kisan kananan yara da ma mata masu juna biyu a kasar.

Gwamnatin Nijar ta kasa yakin da take a kan yaduwar cutar zuwa gida uku da suka hada da neman tallafi da wadatar da al’ummar kasar da maganin rigakafin cutar da kuma tsaftace unguwanni.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...