Nijar ta kama mafarauta ‘yan Najeriya uku

Namun daji

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Nijar ta kama wasu mafarauta guda uku ‘yan Najeriya da ake zargi da satar damun daji a daya daga cikin gandun dajin duniya da ke yammacin Afirka.

An kama su ne a kudu maso yammacin Dosso cikin motar daukar kaya guda biyu shake da hauren giwa da fatun maciji da kan wasu namun dawa da dama da suka kunshi na Bauna da Birai, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

Ana zargin sun yi farautar namun dajin ne ne daga wani babban gandun daji da ya hada kan iyakar Nijar da Burkina Faso da Benin.

Gwamnatin Nijar ta ce ta kuma kama bindigogin farauta da dama, da wasu sinadarai da mafarautan ke dauke da su.

Gandun dajin na Majalisar Dinkin Duniya na da girma sosai wanda kuma ke kunshe damun daji da dama.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...