NFF da kulob din Roma sun kulla yarjejeniya | BBC Hausa

Shugabannin NFF (Amaju Pinnickda) da AS Roma (Jim Pallottane) ne da mataimakansu a wurin taron kulla yar

Hakkin mallakar hoto
NFF

Image caption

Shugabannin NFF (Amaju Pinnickda) da AS Roma (Jim Pallottane) ne da mataimakansu suka halarci taron

Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya NFF ta kulla yarjejeniyar aiki tare da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma mai buga gasar Serie A ta Italiya.

Bisa ka’idojin yarjejeniyar, Roma da Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya za su rika gudanar da harkokin da suka shafi wasanni a ciki da wajen fili, kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana ranar Juma’a.

Bangarorin biyu za su rika taimaka wa juna wajen ci gaban harkokin wasanni da suka hada da shawarwari game da horar da matasan ‘yan wasa daga Najeriya da kuma koyar da kulob-kulob a Najeriya yadda za su rika tafiyar da shafukansu na sada zumunta.

Ita kuma NFF za ta taimaka wa Roma wajen gina nata harkokin a Najeriya.

Kazalika, a watanni masu zuwa jami’an hukumar ta NFF za su yi tattaki zuwa birnin Rome domin ganin yadda kungiyar matasa ta Roma ke gudanar da wasanninsu.

Hakan zai ba su dama wurin gina matasa da kuma kungiyoyinsu a harkar wasanni a gida Najeriya.

Shugaban kungiyar ta Roma Jim Pallotta ya ce tun a 2018 suka fara aiki da Super Eagles yayin gasar cin Kofin Duniya a kasar Rasha.

“Rukunin ma’aikatanmu sun fara aiki tare da Super Eagles a 2018 a shafukan sada zumunta da kuma lokacin gasar Kofin kasashen Afirka, wanda aka fara da maudu’in #ForzaSuperEagles.

“Mu ne kungiya ta farko daga wajen Najeriya da ta bude shafin Twitter cikin harshen Pidgin mai shelkwata a Lagos.”

Kungiyar za ta duba yiwuwar buga wasan bude ido a Najeriya tare da bude makarantar horar da wasanni.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...