Kwanturolan hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) mai kula da rundunar Jibia ta musamman a jihar Katsina, Mustapha Sani, ya gargadi ‘yan Najeriya kan yin balaguro zuwa Jamhuriyar Nijar.
Hakan dai ya zo ne sakamakon rikicin jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Kasar ta Afirka ta Yamma ta fuskanci takunkumi sakamakon kasancewerta karkashin mulkin soja.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis a wani bikin hadin gwiwa da hukumar NIS ta jihar Katsina domin bikin cika shekaru sittin.