Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Alhamis ya bayyana bukatar gwamnatin shugaba Bola Tinubu na kara zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasar Najeriya da Jamhuriyar Cuba.
Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasar, Olusola Abiola, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Shettima ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa mataimakin shugaban kasar Cuba, Salvador Valdez Mesa a fadar De Revolution, Havana.
A halin yanzu Mista Shettima yana kasar Cuba ne domin wakiltar Tinubu a taron shugabannin kasashen G77+ na kasar Sin a birnin Havana na kasar Cuba, wanda ake gudanarwa daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Satumba.
Ya kara da cewa, “Muna matukar girmama kasar Cuba, musamman irin sadaukarwar da kuka yi mana a Afirka.”
Yayin da yake yabawa da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Mista Shettima ya jaddada bukatar kasashen biyu su sake kulla alaka a nan gaba.