
Mutane biyu ne suka ɓace a yayin da aka samu nasarar ceto wasu mutane uku a wani hatsarin jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Gamadio dake jihar Adamawa.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ita tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.
Ladan Ayuba shugaban sashen ayyukan yau da kullum na hukumar NEMA a Yola shi ne ya jagoranci tawagar kai ɗaukin gaggawa tare da mataimakin gwamnan jihar, Kaletapwa Farauta ya zuwa wurin da abun ya faru.
Shugaban karamar hukumar, Christopher Sofore ya yi wa mataimakin gwamnan bayanin abun da ya faru inda ya ce ana cigaba da aikin bincike domin gano gawarwakin mutane biyu.
Mataimakin gwamnan ya sanar da kafa wani kwamitin bincike da ya ƙunshi jami’an tsaro na DSS, ƴan sanda, jami’an kashe gobara, NEMA da kuma na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa domin cigaba da gudanar da aikin gano mutanen biyu.
Ya kuma shawarci hukumomin da abin ya shafa da su samar da rigar kariya tare da tabbatar da cewa ana amfani da su domin kare faruwar irin haka nan gaba.