[ad_1]
Aƙalla mutane biyar ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale akan hanyarsu ta zuwa yankin Ikorudu a jihar Lagos.
Adesina Tiamiyu, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos LASEMA ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce hukumar ta samu kiran kai daukin gaggawa da misalin karfe 5:30 na yamma.
Tiamiyu ya ce wani jirgi mai cin mutane 20 mallakin kamfanin Blue Sea ya nutse a tsakiyar teku akan hanyarsa ta zuwa Ikorudu daga tsibirin da ake kira Lagos Island.
Binciken farko da aka gudanar bai nuna musabbabin faruwar hatsarin ba.
“Abin takaici mutane biyar (mata 4 da kuma namiji daya) aka tabbatar da mutuwarsu kuma tuni aka ajiye gawarwakinsu a dakin ajiye gawarwaki dake babban asibitin Ikorudu,”a cewar Tiamiyu.
[ad_2]