Mutane 7 sun ɓace sanadiyar ambaliyar ruwa a Niger

Aƙalla mutane 7 aka ayyana da sun ɓace a yayin da ambaliyar ruwa ta shanye gidaje da dama da gonaki a ƙananan hukumomin Magama da Mashegu dake jihar Niger.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Juma’a.

Al’ummomin da abun ya shafa sun haɗa da na Sabon Pegi  dake Mashegu da kuma Nassarawa a Magama.

Abdullahi Baba Arah, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger da yake tabbatar da faruwar lamarin ya ce ɗaruruwan gidaje da  hekta mai yawa ta gonaki abun ya shafa.

Ya ce mamakon ruwan sama da ake yi shi ne ya haifar da ambaliyar ruwan.

More from this stream

Recomended