Mutane 10 Sun Ƙone Ƙurmus A Gobarar Tankar Mai A Jos

Akalla mutane 10 ne suka gone kurmus har lahira a ranar, Alhamis bayan da wata tanka dake dauke da mai ta faɗi a mahadar dake kan Titin Bauchi a ƙaramar hukumar Jos North.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Filato, Alfred Alabo ya ce tankar wacce ta kwace ta fadi tare da kamawa da wuta inda ta kone wasu motoci uku da wasu babura masu kafa uku guda biyu.

Alabo ya ce isar jami’an su wurin sun iske gawarwakin mutane 10 da suka kone kurmus inda suka ɗauke su zuwa Asibitin Specialist Hospital Jos.

More from this stream

Recomended