Muna jan hankalin gwamnatin Kaduna kan rushe mana coci – CAN | BBC Hausa

Elrufai

Kungiyar mabiya addinin kirista reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yunkurin gwamnati na rusa cocin Anglican na Saint Geoges da ke Sabon garin Zaria, wadda aka gina a 1908.

An dai ce gwamnati na son rusa cocin ne da manufar fadada wata kasuwa da ke kusa da ita.

Shugaban kungiyar, Reverend John Hayab ya bayyana wa BBC cewa an sha yunkurin rusa majami`ar da nufin fadada kasuwar da ke makwabtaka da cocin ana fasawa saboda tarihinta.

“Yawancin wadanda suke shugabanci a yanzu ba a haife su ba lokacin da aka gina cocin”.

Reverend Hayab ya karyata cewa an bai wa cocin diyya “Muna zaune kawai sai muka ga wasika wai za a rushe coci saboda an biya kudin diyya. Ba bu wanda ya biya diyya”

“Na biyu wasikar kuma ba ta da kwanan wata a jikinta. Shi ya sa muke neman gwamnatin jihar ta Kaduna ta fada mana tana da masaniya kan wannan wasika idan ba haka ba kuma muna son ta hukunta duk mai hannu a al’amarin.”

  • Gobara ta tashi a Majami’ar Notre-Dame a Faransa
  • Da gaske ne gwamnatin Rivers ta rushe masallaci?

BBC dai ta yi kokarin tuntubar Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kaduna, wanda shi ne mai magana da yawun gwamna, Mr Aruwan domin jin nasu bangaren, amma ba a yi nasara ba.

A Najeriya dai al`amuran da suka shafi addini ko ibada , kamar yadda masu lura da la`amura kan ce suna bukatar a yi kaffa-kaffa da su, sakamakon yadda suka haddasa kace-na-ce.

Ko da a `yan kwanakin baya ma, an yi ta kartar-kasa da murza gashin-baki tsakanin al`umar musulmi da gwamnatin jihar Rivers, bayan gwamnati ta share wani wuri da musulmin ke sallar juma`a.

Sai dai har zuwa yanzu dai gaskiyar maganar ta kasa fita. Yayin da musulmi ke cewa masallaci mallakinsu aka rusa, bangaren gwamnati kuma na cewa fili ne na Allah, kuma ba mallakin musulmin ba ne.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...