Mourinho zai koma horarwa a Bundesliga

Mourinho

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon kocin Manchester United, Jose Mourinho, na burin lashe kofi na biyar a wata kasar da bai horas da tamaula ba, wanda hakan ya bayar da kofar kungiyoyin Bundesliga su yi zawarcinsa.

A watan Disambar 2018 ne Manchester United ta sallami Mourinho mai shekara 56, wanda ya ce an yi masa tayin aiki har karo hudu. amma bai amince ba.

Mourinho ya lashe kofin gasar Portugal da Ingila da Italiya da kuma Spaniya a lokacin da ya horar da Porto da Chelsea da Inter Milan da kuma Real Madrid.

Gasar Bundesliga da ta Faransa ce kawai kocin bai horar da kwallo ba daga manyan gasa biyar a nahiyar Turai, inda ake alakanta shi da zuwa Lyon, koda yake daga baya an fahimci ba za ta rabu da Bruno Genesio ba.

Ana hasashen cewar Mourinho zai koma gasar Bundesliga a badi, kuma kungiyar Bayern Munich wadda ake ganin ba za ta ci gaba da aiki da Niko Kovac ba.

Munich wadda take ta biyu a kan teburin Bundesliga tana biye da Borussia Dortmund ta daya, kuma Liverpool ce ta yi waje da Bayern a wasan zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai ta bana.

Mourinho ya ce yana da burin lashe Champions League na uku a wata kungiyar, kuma kofin gasar wata kasa na biyar a tarihi.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...