Mourinho, Tsohon kocin United, zai sha daurin shekara guda

Jose Mourinho drives away after leaving his job as Manchester United manager in December

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Tsohon kocin Manchester United da Real Madrid, Jose Mourinho, ya amince da daurin shekara daya a gidan yari a Spain saboda kauce wa biyan haraji.

Da wahala ya yi zaman gidan yarin saboda ba kasafai kasar Spain ke matsawa kan mutum ya je gidan kason ba idan daurin da aka yi masa bai kai shekara biyu ba.

Spain ta zargi dan kasar ta Portugal da kauce wa biyan haraji na €3.3m

Baya ga daurin je-ka-ka-gyara-halinka, tsohon kocin zai biya tarar €2m.

Laifukan da aka same shi da laifin aikatawa sun shafi rashin bayyana kudin da ya samu daga tallan hotunansa lokacin da yake kocin Real Madrid tsakanin 2011-2012.

An zarge shi da bude hanyoyin kasuwanci daban-daban a tsibiran British Virgin Islands da wasu wurare da ke tallata hotunansa.

masu shigar da kara sun ce ya yi hakan ne da zummar kauce wa biyan haraji.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...