‘Mourinho na gab da barin Man U’ Madrid na son dan Man City

0


Danny Rose

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Danny Rose

‘Yan wasa da ma’aikatan Manchester United suna gani saura shan kaye daya a kori koci Jose Mourinho, in ji Daily Mail.

Dabarun wasa da kuma tsarin zaben ‘yan wasa na baya-bayan nan da kocin dan kasar Portugal ke amfani da su sun kidima ‘yan wasan United, kamar yadda Sun ta ruwaito.

Ita kuwa Sky Sports ta bayar da rahoton cewar Real Madrid tana sha’awar sayen dan wasan gaban Manchester City Raheem Sterling, mai shekara 23, amma ba a wannan bazara ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Raheem Sterling

Real ta shirya domin sake sayen dan wasan gaba Mariano Diaz daga Lyon, in ji El Pais.

Har yanzu Barcelona tana son sayen dan wasan baya kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ranar Laraba, sai dai kulob din ya ce ba zai sayi dan wasan Manchester United dan Faransa ba, mai shekara 25, Paul Pogba, in ji Sport.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alexandre Lacazette

Dan wasan gaban Arsenaldan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 27, yana tunanin makomarsa a Emirates, kamar yadda Le10Sport ta ruwaito.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Danny Rose

Dan wasan bayan Tottenham mai shekara 28 Danny Rose zai ki tayin komawa Paris St-Germain buga wasan aro, in ji Telegraph.

Real Betis ta shirya domin daukar aron dan wasan Barcelona, mai shekara 25 Rafinha on loan, in ji Sport.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here