Melaye ya gaza halartar zaman kotu

[ad_1]








Dino Melaye, sanata mai wakiltar mazabar yammacin Kogi a ranar Litinin bai halacci zaman kotun majistire dake Lokoja ba inda ake tuhumarsa da laifin safarar bindigogi.

Ben Murray-Bruce, sanata dake wakiltar mazabar Bayelsa ta gabas ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter dake fadin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Melaye.

A cewar Bruce anyi garkuwa da Melaye lokacin da yake kan hanyarsa ta halartar zaman kotun a jihar Kogi.

Wani makusancin sanatan, Musa Shu’aibu ya sheda lokacin da aka yi garkuwa da sanatan akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

“A dai-dai lokacin da muke magana yanzu ba musan inda sanatan yake ba,” ya ce .

Melaye na ɗaya daga cikin sanatoci 14 da suka fice daga jam’iyar APC mai mulki.




[ad_2]

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...