Me yasa ‘yan Najeriya ke son komawa Canada?

'Yan Najeriya suna bayyana ra'ayinsu game da zaben 2019

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu ‘yan Najeriya suna bayyana ra’ayinsu game da zaben 2019

Wasu ‘yan Najeriya na tafka muhawara bayan da wasunsu suka ce za su koma kasar Canada saboda daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da hukumar zaben kasar ta yi.

Suna tafka muhawarar ne a shafin sada zumunta na Twitter.

Ba a san wanda ya fara amfani da maudu’in ba, sai dai a halin da yake ciki shi ne maudu’i mafi shahara a shafin Twitter a kan zaben Najeriya wadda hukumar zabe ta Najeriya ta daga zuwa makon gobe.

Maudu’in na cewa saboda fusatar da ‘yan Najeriya suka yi da matakin na hukumar zaben, shi yasa za su fice daga kasar zuwa Canada.

Amma wasu ‘yan Najeriyar na kallon batun ta fuskar barkwanci, kuma sun rika wallafa hotunan da kan sa mutane dariya da nishadi.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Image caption

Shugaban hukumar zabe a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu

Ga wasu daga cikin sakonnin da aka wallafa a shafin na Twitter:

Ye of Canada (@blaisemaen) ya wallafa hoton Atiku Abubakar da tsohon dan takarar mukamin gwamnan jihar Osun da bai yi nasara ba.

Ya nuna kamar mutanen biyu na tattaunawa kan batun na komawa Canada, amma ya sauya masu sunaye, inda ya kira daya John, daya kuma ya kira shi Saki:

John: Abokina ba ka san abin da na gani ba da na isa Canada ba.

Saki: Me ya faru?

John: Sai naga ‘yan Najeriya a ko’ina.

Wani mai suna @PaultwinOkoye ya wallafa wani hoton na wasu jiragen sama masu tarin yawa na tashi daga filin jirgin sama:

Hoton ‘yan Najeriya da ke ficewa daga kasar zuwa Canada 😂😂😂🤣🤣🤣🤣🏃🏃🏃🏃🏃

Shi kuwa @laffbro ya wallafa wani hoton motar bas ta haya da wasu fasinjoji ke kokawar shiga cikinta har ta tagoginta:

Yayin da ‘yan Najeriya suka ji yaron mota na kiran fasinja su tabbata sun shiga motar zuwa Canada da canjinsu na naira 200! 😂😂😂

Shi ma @s_potentials ba a bar shi a baya ba, domin ya wallafa wannan hoton na kasa da sako mai cewa:

Yadda ‘yan Najeriya ke shirin ficewa zuwa Canada a bana.

Sai kuma @YoungSaeed da ya wallafa sakon wasu fasinjoji tare da kayansu a kusa da wata motar haya:

‘Yan Najeriya na barin kasarsu zuwa Canada.

A karshe kuma ga wannan mai suna @psalmuel__ wanda ya ce:

Ina sanar da ‘yan uwana ‘yan Najeriya cewa kuna daf da rasa ni ga kasa mai alamar ganyen maple, wato Canada!

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...