Me ya sa gwamnatin Ganduje ke takun saka da mawakan Kannywood? | BBC Hausa

Ganduje da Naziru da oscar

Kamun da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta yi wa Naziru M. Ahmed ranar Laraba da yamma ya sake tado da sabuwar kura kan rikicin siyasar da yake faruwa a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa sun kama mawakin ne “saboda kalaman batanci” da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Ya kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da mawakin ya musanta.

Sai dai Malam Aminu Saira, dan uwan mawakin, ya gaya wa BBC cewa ‘yan sanda sun sanar da su cewa ‘gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama shi ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar Kano’.

“An kama Naziru ne saboda fitar da wani kundin waka da ya yi mai suna ‘Gidan Sarauta’ da kuma ‘Sai Hakuri’. Mun yi kokari a ba mu belinsa jiya da daddare amma an ki,” in ji Saira — a lokacin Naziru yana gidan yari kafin a sako shi.

Hasalima, a cewarsa, an fitar da kundin wakar ne shekara hudu da suka gabata.

Tuni dai Naziru ya bayyana a gaban wata kotun Majistare a birnin Kano. An bada belinsa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da zasu tsaya masa, wadanda dole su kasance ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune.

Mun yi kokarin jin ta bakin shugaban hukumar tace fina-finan, Isma’ila Na’abba Afakallah, amma bai amsa kiran wayar da muka yi masa sau da dama ba. Kazalika bai yi martani kan sakon text da na WhatsApp din da muka aika masa ba.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ambato shi yana musanta cewa siyasa ce ta sa ake cin zarafin mawakan yana mai cewa sun keta dokokin hukumar tace fina-finai ne.

‘Alaka da Sarki Sanusi da Kwankwasiyya’

Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga rarraba masarautarsa zuwa gida biyar.

Kazalika, mawakin fitaccen dan kungiyar Kwankwasiyya ne, wato bangaren siyasar jam’iyyar hamayya ta PDP da tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta ne.

A 2015 dai tsohon gwamna Kwankwaso ya yi ruwa ya yi tsaki wurin ganin Gwamna Ganduje ya ci zabe – kuma sun yi nasara. Amma daga bisani sun raba gari.

Aminu Saira na ganin cewa kama kanin nasa bai rasa nasaba da siyasa, domin kuwa, a cewarsa, “idan dan uwan nasa ya yi waka ‘yan kasuwa yake sayarwa. Don haka su ya kamata a tuhuma. Kazalika kamfanin da yake buga wakar “nawa ne ba na Naziru ba, don haka idan suna da matsala da wakokin ni ya kamata su tuntuba.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumar tace wakoki da fina-finai ta Jihar Kano ke kama jarumai da mawakan Kannywood ba.

Wasu jarumai da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood na ganin a yanzu hukumar ta mayar da hankali ne wajen musgunawa wadanda ake jin suna adawa da gwamnati.

Kafin kamun da aka yi wa Naziru sarkin waka, hukumar tace fina-finan ta kama Sadiq Zazzabi da kuma a baya bayan nan Sunusi Oscar bisa zarge-zarge da suka hada da saba kai’dar aiki.

A takaice, hukumar ta ce ta kama Sanusi Oscar ne saboda “ya fitar da wata waka wadda ke nuna badala”, yayin da shi kuma Sadiq Zazzabi aka kama shi saboda zargin saba wa dokar da ta ce wajibi ne duk sabuwar wakar da za a fitar sai an gabatar da ita ga hukumar don tacewa da kuma samun sahalewarta.

Za mu sanya kafar wando daya da Afakallah

Sai dai jarumi kuma mai bayar da umarni, Falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa kamen da aka yi wa dukkan mawakan uku na da alaka da siyasa.

Hakkin mallakar hoto
Instagram/real_dauda_kahutu_rarara

Image caption

Wasu ‘yan Kannywood sun yi zargin cewa Rarara shafaffe ne da mai shi ya sa ba a daure shi ba

“Da farko ya kamata ka sani cewa dukkan wadannan mawaka ‘yan PDP ne kuma sun yi shura wajen caccakar gwamnatin Kano ta APC. Idan har da gaske ne cewa an kama su ne domin sun saba doka, me ya sa ba a taba kama Dauda Kahutu Rarara ba? Babu wanda ba ya zagi a cikin wakarsa amma tun da dan jam’iyyar APC ne sun kasa kama shi.”

Tuni dai fitattun jarumai irin su Adam Zango da Mustafa Naburaska suka bayyana cewa sun dakatar da yin fim a jihar Kano, har sai lokacin da gwamnati ta daina cin zarafin ‘yan fim.

Kazalika, jarumai irin su Sani Danja da Ali Nuhu sun yi kira a bi a hankali kan yadda ake kama mawaka da ‘yan fim.

Su ma jaruman fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya ba a bar su a baya ba wajen sukar gwamnati kan kamun da aka yi wa mawakan Kannywood.

Fitacciyar jarumar nan Kate Henshaw ta gargadi hukumar tace fina-finan jihar Kano kan musgunawa mawaka.

Su ma masu sharhi a masana’antar Kannywood sun ce wadannan kame-kame take hakkin dan adam ne da ‘yancin fadin albarkacin baki, kuma za su iya jawo mummunar gaba a masana’antar.

Muhsin Ibrahim mai nazari ne kan fina-finan Kannywood, kuma ya shaida BBC cewa “kama mawaĆ™a da gwamnatin Kano take abin takaici ne ga Kannywood. Yana Ć™ara jawo rarrabuwar kai da gaba a tsakanin mutanen masana’antar wadda dama tuni alaĆ™a ta yi tsami a tsakaninsu.

Ya kara da cewa “hakan zai kashe bunĆ™asar masana’antar da kuma sa tsoro a zukatan mawaĆ™a da sauran mutane. A hankalce, ba dole ne kowa ya bi bayan gwamnati mai ci ba. Cusgunawa mawaĆ™a na nufin a daina adawa, wadda kuma ba zai yiwu ba.”

Sai dai ya yi kira ga mawakan da su bi doka “su kuma yi adawa mai tsafta da kuma hankali”.

Amma Falalu Dorayi ya ce idan har gwamnati ta ci gaba da amfani da hukumar tace fina-finai wurin cin zarafin ‘yan fim, to ba za su yi kasa a gwiwa wajen adawa da ita ba.

“Muna kira ga shugaban hukumar tace fina-finai ya sani cewa ya daina bari ‘yan siyasa suna amfani da shi wurin cimma burinsu. Amma idan ba haka ba, za mu sanya kafar wando daya da shi kuma za mu yi galaba a kansa kamar yadda muka yi a kan magabacinsa,” in ji Dorayi.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...