Mayaƙan ISWAP sun sace yara mata da maza 20 a Jihar Borno

Masu iƙirarin jihadi da ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe mutum biyu tare da sace wasu yara 20 a kusa da garin Chibok na Jihar Borno ranar Alhamis.

Wani shugaban yankin ya faɗa wa manema labarai cewa maharan sun afka wa garin Piyemi, inda suka yi awon gaba da mata 13 da maza bakwai.

A cewar mazauna yankin, mayaƙan na Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun afka wa garin ne da rana cikin kakin sojoji suna harbe-harbe tare da sace kayayyakin shaguna, sannan suka dinga ƙona gidaje.

“Sun harbe mutum biyu sannan suka sace yara mata 13 da maza bakwai, shekarunsu 12 zuwa 15,” kamar yadda mazaunin yankin Samson Bulus ya faɗa wa AFP.

Wani mai suna Silas John ya ce “maharan sun zuba yaran 20 cikin wata motar a-kori-kura da suka ƙwace a ƙauyen kuma suka shiga daji da su”.

More News

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...

Nigerian military eliminate 42 terrorists in North East

The Defence Headquarters says troops of Operation Hadin Kai have neutralised 43 terrorists, arrested 20 and rescued 63 kidnapped victims within three weeks. The Director,...