Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe wani babban jami’in ɗan sanda a arewacin jihar Borno.
A cewar wasu rahotanni mayaƙan sun saɗaɗa cikin garin New Marte inda suka farma wani ma’aikacin lafiya amma Allah ya bashi sa’ar tserewa.
Ma’aikacin lafiyar ya garzaya ofishin ƴan sanda domin sanar da su abun da yake faruwa.
Bayan samun kiran kai ɗaukin gaggawa ne DPO ɗin chaji ofis ɗin ya jagoranci jami’ansa domin bin sahun su amma cikin rashin sani sun faɗa kwanton ɓaunar da ƴan bindigar suka yi musu.
Wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin “Mayaƙan Boko Haram sun shiga New Marte jiya kuma sun kashe DPO tare da jikkata wasu mutane biyu.” Ya ce.
A cewar wata majiyar wanda ɗan bijilante ne a garin ya ce “Wallahi abun akwai takaici.Mun rage masa hanya lokacin da muke dawowa daga Dikwa wata rana. ya ce zai je ya ga iyalansa a Maiduguri.”