
Mayakan kungiyar ISWAP su 73 tare da iyalinsu ne suka mika kansu ga sojojin shiya ta ɗaya na rundunar Operation Haɗin Kai dake Borno.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan al’amuran tsaro da suka shafi yankin tafkin Chadi, 42 daga cikin yan ta’addar tare da iyalinsu da suka haɗa da maza 4 mata 10 da kuma kananan yara 28 da suka fito daga ƙauyukan Bula Bello, Zaramari da kuma Garno sun miƙa kansu a ranar Laraba.
Sojojin bataliya ta 202 dake Bama su ne suka karbe su.
Bayanin na Zagazola ya cigaba da cewa maza biyu da mata 7 da kuma yara 9 daga ƙauyukan Ngauri, Siraja da kuma Nbellana sun miƙa kansu ga dakarun bataliya ta 152.
Zagazola ya kara da cewa mambobin ISWAP 9 da manyan mata biyu daga Ukuba sun miƙa kansu ga rundunar soja dake Gwoza.
Wasu majiyoyi dake rundunar sojan Najeriya ta ce ana cigaba da tantance tsofaffin ƴan ta’addar kafin a miƙa su ga hukumomin da su ka kamata.