Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno.

Mayaƙan biyu Awana Malam Kurama da Tahir Isa sun miƙa kansu ne ga sojojin rundunar Operation Haɗin Kai dake Bama bayan da suka  gudo daga sansaninsu dake ƙauyen Bahrain a Dajin Sambisa ranar 8 ga watan Mayu.

Wasu majiyoyin jami’an tsaro sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa mayaƙan biyu sun miƙawa jami’an tsaro bindiga guda ɗaya ƙirar AK-47 da harsashi guda 10 kuɗi ₦29,000 da kuma kekuna guda biyu.

Jami’an soja na cigaba da tsare mutanen inda ake cigaba da ɗaukar bayanansu.

More from this stream

Recomended