Matatar man fetur ɗin Dangote ta rage ₦20 a farashin litar man fetur

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man  fetur daga kan ₦990 ya zuwa ₦970 a kan kowace lita.

Hakan na nufin matatar ta rage ₦20 kan farashin da take sayarwa da manyan dilalan man fetur.

A farkon wannan watan ne matatar ta sanar da cewa za ta riƙa sayarwa da ƴan kasuwa litar man fetur kan kuɗi ₦990..

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi   ta ce ragin  na ₦20 zai taimakawa ƴan kasuwar ƙara samun riba.

Anthony Chijiena mai magana da yawun matatar ya ce sun ɗauki matakin ne domin godewa ƴan Najeriya kan goyon baya da suke basu na tabbatuwar matatar man fetur ɗin.

More from this stream

Recomended