Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus tare da ficewa daga jam’iyar APC ya zuwa PDP

0

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya sauka daga kan mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyar APC inda ya koma jam’iyar adawa ta PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan ya kasance makusancin tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya koma jami’yar PDP kwanakin da suka wuce.

Murabus din nasa na bazata baya rasa nasaba da yunkurin tsige shi da wasu yan majalisar dokokin jihar 31 suke shirin farawa a ranar Litinin.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Agusta wacce ya aikawa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yayi murabus din ne saboda ra’ayi mabanbanta da suka gaza cimma dai-dai to akan su.

Abubakar ya ce ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin sun samu dai-daito amma hakan ya ci tura.

A makon da ya gabata ne Abubakar ya sanar da rundunar ƴansanda cewa rayuwarsa na fuskantar barazana.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here