Manhajojin Facebook sun gamu da cikas

Facebook

Kamfanin shafin Facebook na fuskantar matsala mafi tsanani a tarihinsa, inda ake cin karo da matsaloli wajen aiki da wasu daga cikin manhajojinsa na intanet a fadin duniya.

Sai dai kamfanin ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.

Baya ga ainahin shafin na Facebook shi kansa, manhajar Messenger da Instagram su ma sun gamu da cikas.

Ba a dai gano abin da ke haddasa matsalar ba, wadda ta fara tun kusan karfe hudu na yamma agogon GMT, wato biyar na yammacin jiya a gogon Najeriya da Nijar.

Masu amfani da shafin Facebook sun iya bude shi amma kuma ba sa iya sanya abubuwa a shafin.

Manhajar Messenger ta waya tana aiki ga wasu amma kuma wasu ba ta yi musu aiki, amma kuma manhajar ta Kwamfutar tebur ba ma a samunta.

Matsalar dai ba ta shafi WhatsApp ba.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ćłan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...