Man City ta fi kowacce kungiya zura kwallaye a Turai

Manchester City

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester City ita ce ta farko da ta ci kwallo sama da 100 a tsakanin manyan kungiyoyin da ke buga gasar Lik-Lik ta Turai ta kakar 2018/19.

A ranar Lahadi City ta ci Huddersfield 3-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier, kuma Danilo ne ya fara cin kwallo, wadda ita ce ta 100 da ta zura a raga a dukkan fafatawa da ta yi a bana.

Daga baya ne ta kara biyu a karawar ta hannun Raheem Sterling da kuma wadda Leroy Sane ya ci, jumulla City tana da kwallo 102 da ta zura a raga a wasannin da ake yi.

‘Yan wasa 17 ne suka ci wa City kwallo 102 a kakar bana, inda Sergio Aguero da Gabriel Jesus kowanne ya ci 14, sai Sterling mai 12 da kuma Sane wanda ya ci 11.

Tun bayan da Crystal Palace da Leicester City suka yi nasara a kan City a Premier, kawo yanzu ta dura kwallo 22 a raga a wasa hudu da ta buga.

A kakar 2013/14 City ta lashe kofin Premier ta kuma zura kwallo 156 a karkashin jagorancin Manuel Pellegrini a dukkan gumurzun da ta yi a kakar.

Paris Saint-Germain ce ke biye da City a yawan cin kwallaye a bana, bayan da ta zura 90 a raga, sai Barcelona ta uku mai guda 78.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...