Toshuwar ministar harakokin mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan wadda aka fi sani da Mama Taraba ta nemi yan Najeriya da suyi mata addu’a kan aikin tiyata da za a yi mata a kokon gwiwarta.
Alhassan ta fadi rokon nata ne cikin wani gajeren sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
“Na shirya domin yimin aikin tiyatar sauya kokon gwiwa.Dan Allah ina bukatar kuyi muni addu’a. Allah ya ƙaddara saduwar mu,Amin,”a cewar sakon da ta wallafa.
Shekarar da ta gabata dai an ta rade-radin tsohuwar ministar bata da lafiya bayan da aka shafe watanni ba a ganinta a bayyanar jama’a.
Daga bisani Alhassan tayi karin haske kan cewa ta kwanta biyar wani ciwo da ta bayyana ba.