Malamin da ya kashe dalibinsa zai sha hukuncin rataya

rataya

Wata kotu a tanzaniya ta yanke wa wani malamin makaranta mai shekara 51 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe wani dalibi mai shekara 14 da ya yi ta sanadin dukansa.

Respicius Mtazangira ya zane tare da dukan Sperius Eradius da wani abu mara kaifi a makarantarsu da ke Bukoba a arewa maso yammacin Tanzania a watan Agustan bara, yana mai zargin yaron da satar wata jaka da aka nema aka rasa.

Sperius dai ya musanta zargim, amma duk da haka Malam Mtazangira sai da ya musguna masa.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, alkalin babbar kotun Lameck Mlacha ya samu Malam Mtazangira da laifin kisan kai, amma ya wanke wani malamin daban Heriet Gerald.

Wasu shaidu tara da suka hada da dalibai tun ba da shaida yayin sauraron karar. Wani rahoton asibiti da aka gabatar wa kotun ya nuna cewa dukan ne ya jawo wa yaron mutuwa.

An ruwaito lauyan Malam Mtazangira yana cewa akwai yiwuwar ya daukaka kara kan hukuncin.

Rabon Tanzania da yanke hukuncin kisa tun shekarar 1994.

Shugaba John Magufuli ya bayyana a shekarar 2017 cewa ba ya goyon bayan yanke hukuncin kisa.

“Na san akwai mutanen da aka same su da laifin kisan kai kuma suna jiran hukuncin kisa, amma ina rokon kar ku ba ni jerin sunayen don yanke hukunci saboda na san tashin hankalin da ke cikin hukuncin kisa,” a cewarsa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...