Maki biyu ne suka saura tsakanin City da Liverpool

Sergio Aguero

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester City ta lallasa Arsenal da ci 3-1 a wasan mako na 25 a gasar cin kofin Premier da suka fafata a Ettihad a ranar Lahadi.

City ta ci kwallayen ne ta hannun Sergio Aguero wanda ya ci uku rigis, kuma karo na 10 da ya yi wannan bajintar a Premier, Alan Sherer ne ke kan gaba da 11 a tarihi.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannu Laurent Koscielny tun a minti na 11 da fara tamaula.

Da wannan sakamakon City ta koma ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool ta daya a kan teburi mai maki 61, wadda za ta yi wasa ranar Litinin.

Arsenal kuwa ta koma ta shida a teburi, bayan da United ta doke Leicester City a ranar Lahadi ta koma ta biyar da tazarar maki biyu tsakaninta da Chelsea ta hudu mai maki 50.

Sai a ranar Litinin ne West Ham United za ta karbi bakuncin Liverpool a karshen wasan mako na 25 a gasar ta cin kofin Premier.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...