Majalisar koli ta Najeriya ta amince da karamin albashi naira dubu 27

Majalisar kasa a Najeriya
Hakkin mallakar hoto
Presidency

Majalisar koli ta Najeriya ta amince da naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi da kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu.

Majalisar ta kuma tsayar da naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan Tarayya.

Shugaba Muhammadu buhari ne ya jagoranci taron majalisar a fadarsa a ranar Talata wacce ta kunshi tsoffin shugabanni da tsoffin alkalan alkalan Najeriya da kuma gwamnoni.

Za a mika kudirin ga majalisa a ranar laraba domin ta amince kamar yadda ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana.

Ya ce majalisar ta cimma matsayar ne bayan nazari kan matsayar da kwamitin diba bukatar karin albashin ya yanke ta naira dubu 30 da dubu 24 da gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biya da kuma naira dubu 22,700 da gwamnoni suka ce za su iya biya.

Karin bayani na tafe..

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...