Majalisar malamai ta yi watsi da sakamakon zaben Kano

0

Majalisar malamai ta jihar Kano ta yi watsi da zaben gwamnan jihar da aka sake a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, ta bayyana shi a matsayin fashin damokradiyya.

A wani jawabi dauke da sa hannun Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, Shugaban kungiyar, yace majalisar malamai ta Kano sun yi Allah wadai sannan sun yi watsi da fashin damokradiyya da mutanen Kano suka fuskanta a kwanan nan, da sunan zaben gwamna.

Dr. Kofar Mata ya bayyana cewa,
“kamar kowane mai son zaman lafiya a Kano, masu kula da zabe da dama na gida da wajen kasar sun yi korafin cewa zaben wanda ya kamata ya zama na gaskiya da amana, da kuma zaman lafiya ya zamo cike da karya doka.”

Majalisar malaman a cikin jawabin ta jero tarin karya doka da aka yi kamar haka: “tarin siyan kuri’u daga yan siyasar APC, yaduwar rikici wanda jam’iyya mai mulki ta shirya kuma ta dauki nauyi domin razanarwa da kuma tozarta masu zabe da jami’an PDP.”

Har ila yau majalisar tayi korafi akan yadda aka wofantar da na’urar tantance katunan zabe, wanda a cewarta hakan kwace yancin masu zabe ne da kuma hadn bakin jami’an INEC da wasu hukumomin tsaro.

Daga karshe sun yi kira ga gwamnatin tarayya da dukkanin hukumomin da abun ya shafa, da su yi kokarin kwato wa mutane yancinsu domin tabbatar da damokradiyyar kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here