Majalisar dokokin Jigawa ta dakatar da shugabannnin ƙananan hukumomi uku

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomi uku kan zargin yin tafiya kasar waje ba tare da izinin majalisar dokokin jihar ba da na bangaren zartarwa.

Shugabannin da aka dakatar sun haɗa da Mubarak Ahmad na ƙaramar hukumar Birniwa sai Rufa’i Sanusi na Gumel da kuma Umar Baffa na ƙaramar hukumar Ƴankwashi.

Ana zargin shugabanni uku ne da tafiya kasar Rwanda ba tare da izini ba.

Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan da shugaban kwamitin ƙananan hukumomi, Aminu Zakari Tsubut ya gabatar da kudirin dakatar da shugabannnin.

Ya ce gabanin tafiyarsu majalisar ta bayar da umarni ga shugabannin ƙananan hukumomi da kada su yi tafiya ko ina saboda shirye-shiryen kasafin kuɗin shekarar 2024 da kuma gabatar da shi gaban majalisar da gwamna zai yi.

Har ila yau majalisar ta kafa kwamiti karkashin shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Muhammad Dansure da ya gudanar da bincike kan lamarin kana ya miƙa rahoto cikin makonni huɗu.

More from this stream

Recomended