Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, zai bayyana sunayen wadanda aka nada a matsayin ministoci a zauren majalisar na wannan mako.
A ranakun Talata da Laraba da Alhamis ne ake gudanar da zaman taron majalisar dokokin kasar biyu.
An dai tada husuma a kan jinkirin da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen kafa majalisar ministocin sa watanni biyu bayan rantsar da shi.
A wani sabon gyara ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, dole ne shugaban kasa da gwamnoni su mika sunayen wadanda aka zaba a matsayin ministoci ko kwamishinoni cikin kwanaki 60 da rantsar da su domin tabbatarwar majalisar dattawa.