Majalisar Dattawan Najeriya ta maka Buhari kotu kan Onnoghen

Bukola Saraki da shugaba Buhari

Majalisar Dattawan Najeriya ta shigar da kara a kotun kolin kasar kan batun dakatar da Babban Alkalin kasar.

Majalisar wadda ta yi niyyar zama a ranar Talata 29 ga watan Janairu, ta dage zaman saboda karar da ta shigar.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya fitar Yusuph Olaniyonu a shafin ofishin shugaban majalisar dattawa na Twitter, ta bayyana cewa sun shigar da karar ne a kotun koli.

Suna neman kotun ne da ta yi masu bayani a kan ko shugaba Buhari na da hurumin cire Mista Onnoghen.

Sanarwar ta bayyana dage zaman da aka shirya yi a ranar Talata saboda dama a kan batun cire Onnoghen za a yi.

A halin yanzu tunda batun na a gaban kotu sun fasa zaman saboda ba a tattauna batu idan yana a gaban kotu.

Cire Alakalin Alakalan Najeriya da Buhari ya yi na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce daga cikin Najeriya da kuma wajen kasar, inda kan lauyoyin kasar ya rabu, wasu na goyo baya wasu na Allah-wadai.

Fadar shugaban kasa ta daure fuska kan rashin jin dadin al’amarin da Amurka da Birtaniya suka nuna, inda ta bayyana cewa ba za ta amince da katsalandan daga kasashen waje ba.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...