Mai shari’a Walter Onnoghen ya daukaka kara

Justice Walter Onnoghen

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan shi ne karon farko da aka gurfanar da Alkalin Alkalai a Najeriya a gaban kotu aka kuma yanke masa hukunci

Tsohon Babban Mai shari’a na Najeriya na baya bayan nan Justice Walter Onnoghen ya daukaka kara a kan hukuncin da kotun da’ar ma’aikata ta yanke masa kan laifin kin bayyana biyar daga cikin asusun bankunansa wadanda ke dauke da tarin kudaden waje.

Onnoghen ya gabatar da korafe-korafe guda 16 a gaban kotun daukaka karar a Abuja, jim kadan bayan da kotun da’ar ma’aikatan ta yanke masa hukunci ranar Alhamis.

A daya daga cikin korafe-korafen da ya gabatar ya kafe cewa bai taba amsa laifin cewa ya aikata laifukan da kotun ta zarge shi da su ba, kamar yadda kotun da’ar ma’aikatan ta ce.

Takardar daukaka karar ta kara da cewa, ”Mai daukaka karar (onnoghen) bai amsa laifin kin bayyana dukiyarsa ba daga shekara ta 2005 a matsayinsa na mai shari’a na kotun koli.

”Mai daukaka karar kawai ya bayyana cewa bai bayyana ba ne a shekara ta 2009 kamar yadda aka bukata, saboda ya manta, kuma nan da nan ya bayyana bayan da ya gano hakan.”

Justice Onnoghen ya kuma ce kotun da’ar ma’aikatan ta yi kuskure a tsarin shari’a, kan korar korafin da ya shigar na kalubalantar ikonta na yi masa shari’a, wanda hakan ya keta haddin shari’a.

Haka kuma ya ce kotun ta yi kuskure a tsarin shari’a, kan korar bukatarsa da ta yi wadda a ciki ya nemi alkalin kotun da ya dakatar da yi masa sharia’a bisa zargin nuna bambanci ko san zuciya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Lauyoyi masu kare Justice Walter Onnoghen a yayin wani zama na kotun da’ar ma’aikata

A takardar daukaka karar, Justice Onnoghen ya gabatar da bukatar kotun daukaka karar ta bayar da damar sauraran karar da ya daukaka, sanna kuma ta yanke hukuncin cewa kotun da’ar ma’aikatan ba ta da hurumin sauraren wannan shari’a tasa.

Bugu da kari ya bukaci kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin da waccan kotun ta yi masa, kana ta wanke shi kuma ta sallame shi, baya ga wasu bukatun kuma.

Ita dai kotun da’ar ma’aikatan ta samu Mai shari’a Onnoghen da laifi, ta kuma cire shi daga mukamin babban mai shari’a na Najeriya, da kuma mukamin shugaban hukumar da’ar ma’aikata(CCB).

Haka kuma ta haramta masa rike wani mukami na gwamnati a tsawon shekara 10, baya ga umartarsa da ya mika dukkanin asusun banki biyar wadanda bai bayyana mallakarsu ba a tsakanin 2009 da 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu sun yi zargin cewa shari’ar ta Onnoghen tana da alaka da siyasa, saboda an fara ta ne gab da babban zaben kasar

Dakatar da Onnoghen a can baya ya jawo ce-ce-ku-ce da dama a Najeriya, inda har kungiyar lauyoyin kasar ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen.

Kungiyar ta bukaci mambobinta da su kaurace wa kotu har na tsawon kwana biyu, umarnin da wasu suka bi wasu kuma suka yi burus da shi.

Haka kuma a lokacin dakatarwar, babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Tarayyar Turai sun yi Allah-wadai da dakatar da shi.

Shugaba Buhari dai ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da’ar ma’aikata wacce ta same shi da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi mukamin alkalin alkalan a shekarar 2017.

An zargi Shugaba Buhari da katsa-landan a harkokin shari’a saboda gurfanar da Onnoghen a kotun, ko da za a kalubalanci sakamakon zabensa a kotun koli, inda ake ganin Onnoghen a matsayin barazana ga nasarar ta Buhari idan yana kan matsayinsa na Babban Mai shari’a na kasar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...