Connect with us

Hausa

Mai kudin duniya zai yi takara da Donald Trump

Published

on

Michael Bloomberg (file pic)

Hakkin mallakar hoto
AFP

Mai kudin duniya na 14, Michael Bloomberg yana sake sansana kujerar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Democrats.

Attajirin wanda tsohon magajin garin birnin New York ne ya ce yana da shakku wajen mutanen da suke son fitowa talkara domin ba za su iya kayar da Donald Trump ba a zaben 2020.

Ana sa ran dan kasuwar mai shekara 77 zai gabatar da tsare-tsarensa a ranar Juma’ar nan domin neman cin zaben cikin gida da za a yi a Alabama.

To sai dai shugaba Trump ya yi wa Michael Bloomberg ba’a, inda ya ce ” Idan akwai mutumin da nake son takara da shi shi ne Michael wanda karamin alhaki ne.”

Mutum 17 ne dai ke takarar kujerar shugabancin a jam’iyyar Democrat.

Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, da Senator Elizabeth Warren da Senator Bernie Sanders su ne a gaba-gaba.

Hakkin mallakar hoto
Chip Somodevilla/Getty Images

Image caption

Bernie Sanders da Joe Biden da Elizabeth Warren

Facebook Comments

Hausa

Tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Gaza ya samu cikas | BBC Hausa

Published

on

Fireball

Hakkin mallakar hoto
AFP

Israila ta kaddamar da sabbin hare-hare kan mayakan Falasdinu bayan da aka samu sabbin hare-haren roka daga Gaza kwana daya bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kafafen watsa labaran Falasdinawa sun ce makamai masu linzami sun fada kan wasu wurare mallakar kungiyar mayaka ta Palestinian Islamic Jihad (PIJ) da safiyar Juma’a, abin da ya janyo raunata mutum biyu.

Hakan dai na zuwa ne bayan harba wa Israi’la wasu makaman roka ranar Alhamis, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar PIJ ta ayyana.

Rikici tsakanin Israila da Falasdinawa dai ya kara rincabewa bayan da Israila ta kashe babban kwamandan kungiyar PIJ ranar Litinin.

Isra’ila ta ce Baha Abu al-Ata ‘hadari’ ne kasancewarsa mutumin da ya kitsa kai wa Israila harin roka na baya-bayan daga Gaza.

Fiye da rokoki 450 ne aka harba kan Israila, inda ita kuma ta kaddamar da hare-haren sama a kan Gaza a kwanaki biyu da suka kwashe suna fafatawa.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Najeriya ta yi fatali da bukatar makwabtan kasashe na bude iyakokinta

Published

on

Bisa dukan alamu, Ministocin Kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da suka bukaci bude iyakokin Najeriya da aka rufe tun watan Agustan bana cikin gaggawa, sun fice cikin fushi daga taron da Wakilan Gwamnatocin Kasashen da ke Makwabtaka da Najeriya suka yi a Abuja akan halin da kasashen suka tsinci kansu tun bayan rufe iyakokin Najeriya,domin kuwa Ministan Kula da harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama ya karanata wa Manema Labarai Jawabin bayan taron daga shi sai ‘yan’uwansa na cikin gida.

Kasar Nijar da ke Makwabtaka da Najeriya ta bangaren Arewa ta bayana cewa rufe iyakokin na kasa, ya jawo mata asarar makudan kudade da yawan su ya kai CEFA miliyan 40, kimanin dalar Amurka miliyan 67, Kwatankwacin fiye da Naira miliyan 24 a Kudin Najeriya.

Ministan Kula da Harkokin Cikin gida na Nijar Mohammed Bazoum da ya fice kafin a gama taron ya ce Najeriya ta dauki mataki mai zafi na rufe kan iyakokin ta da Kasashen uku ne a bisa abinda ta kira matsalolin da ta ke fuskanta na fasa kwabri, su ma kansu Nijar wanan matsala tana shafan su, shi ya sa a yau suka taru domin lalubo mafita wacce ba za ta cutar da kowace kasa ba.Saboda matsalar fasa kwari ta addabi kasashen da ke makwabtaka da Najeriyan ne duka.

To saidai Karamin Ministan Hulda da Kasashen waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada ya bayyana wa manema labarai cewa wuni muhimmin mataki da taron ya dauka shi ne na nada wani komiti na musamman da ke dauke da jami’an Kwastan, da na jami’an Shige da Fice,da na Hukumomin tsaron kasashen uku, da zai yi rangadi da sintiri a kan iyakokin kasashen sannan ya bada rahoto da Najeriya za ta duba yiwuwar bude iyakokin ta.

Amma ga mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum Aminu Jumare yana ganin ba a bi dokokin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wajen rufe iyakokin Najeriya ba.

Nan da makonni biyu na gaba Komitin Kula da harkokin tsaro za ta sake wani taro a Abuja babban Birnin Najeriya.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Messi zai buga wa Argentina kwallo ranar Juma’a

Published

on

Lionel Messi

Hakkin mallakar hoto
Quality Sport Images

Image caption

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin

Lionel Messi na cikin tawagar da za ta wakilci kasar Argentina a wasan sada zumunci da za ta fafata da Brazil a kasar Saudiyya ranar Juma’a.

Wannan ne karon farko da dan wasan zai fito a wasa irin wannan tun bayan korarsa daga filin wasa a gasar Copa America a fafatawar kasarsa da Chile cikin watan Yuli.

An dakatar da dan wasan na Barcelona, mai shekara 32, har tsawon watanni uku bayan da ya ayyana cewa ana magudi a gasar.

Hakazalika dan wasan Aston Villa Douglas Luiz a karon farko na cikin tawagar da za ta wakilci Brazil a wasan.

Wannan shi ne karo na farko da kasashen biyu biyu za su yi wasa tun bayan da Brazil ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan kusa da na karshe a gasar Copa America.

Brazil ta kasa cin nasara a wasanni hudu tun lokacin, da ta sha kaye a hannun Peru da ci 1-0 a watan Satumba, yayin da Argentina ta samu nasara a wasanni hudu a lokacin da aka dakatar da Messi, inda ta doke Ecuador 6-1 a watan da ya gabata.

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, amma ana ganin za a iya dakatar da wasan saboda rikicin da ke faruwa a Isra’ila.

Ita kuwa Brazil za ta kara da Koriya ta Kudu a birnin Abu Dhabi ranar Talata, wanda zai kasance wasansu na karshe kafin fara wasannin share fagen shiga Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 da za fara a watan Maris.

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited