Madrid za ta gabatar da Luka ranar Laraba

Luca Jovic

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid za ta gabatar da sabon dan wasan da ta dauko Luca Jovic gaban magoya bayanta a Santiago Bernabeu ranar Laraba.

A ranar dan wasan zai fara sa rigar Real Madrid, sannan ya shiga fili ya yi wasa da tamaula, idan ya gama ya gana da ‘yan jarida.

Madrid ta dauko Luka Jovic daga Eintracht Frankfurt kan yarjejeniyar shekara shida, wato kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2025 a Bernabeu.

Jovic ya koma Eintracht buga wasa aro daga Benfica a shekarar 2017, inda ya ci kwallo 17 a wasa 32 a Bundesliga da guda 10 da ya zura a raga a wasa 14 da ya buga a Europa League.

A watan Maris Real ta sanar da daukar Eder Militao daga Porto, kuma dan wasan mai shekara 21, shi ne na farko da ya koma Bernabeu tun karbar aiki karo na biyu a Bernabeu.

Haka kuma Real ta dauko Eden Hazard daga Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar, kuma a ranar Alhamis za ta gabatar da shi gaban magoya bayanta.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...