Ma’aikatun Amurka sun kwana 22 a rufe

A protester holds a sign signifying hundreds of thousands of federal employees who won't receive salaries as a result of the partial government shutdown. Washington Jan 10 2019
Hakkin mallakar hoto
Reuters

Mako hudu ke nan tunda gwamnatin Amurka, karkashin Donald Trump, ta rufe wasu ofisoshin gwamnati a fadin kasar.

Wannan lamarin ya janyo dakatar da ayyukan gwamnati, lamarin da ya shafi ayyukan yau da kullum, kuma ma’aikata da dama basa samun albashi.

Ma’aikata dubu dari takwas matsalar ta shafa, kuma shugaban Amurkan ya yi kashedin zai sake daukar wasu matakan idan majalisar kasar ba ta mika masa kudden gina wat katang a kan iyakar kasar da Mexico ba

Rabon da Amurkawa su ga irin wannan matsalar dakatar da ayyukan gwamnati tun 1995 lokacin mulkin Bill Clinton inda majalisar kasar a karkashin jagorancin kakakinta Newt Gingrich suka kasa cimma matsaya.

Wannan takardamar ta yanzu da aka fara kwana hudu kafin bikin Kirsimeti kawo yanzu, ya shiga kwana na 22 – kuma shi ne mafi tsawo a tarihin siyasar kasar.

Batun da ya janyo wannan takardamar shi ne na gina wata katanga da shugaba Trump ya ce zai rage kwararar makamai da hodar iblis da kuma kungiyoyin masu aikata manyan laifuka daga shiga kasar ta iyakar ksar da Mexico.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Shugaba Trump ya ce gina katangar zai rage masu aikata manyan laifuka daga shiga kasar daga Mexico

Kin amincewar da ‘yan jam’iyyar Demokrat suka yi na sakin baitulmalin kasar ga shugaba Trump ya harzuka shi, inda ya yi gargadin zai yi shelar ko ta baci.

Dubban daruruwan ma’aikatan gwamnati sun ci gaba da zuwa wajen aiki babu albashi.

Ma’aiktan sun hada da jami’ian tsaro a filayen jiragen saman kasar, da kuma jami’an hukumar FBI mai binciken manyan laifuka.

Duk da kiraye-kirayen da Mista Trump ke yi na ‘yan jam’iyyar Demokrat su hau teburin tataunawa, babu alamar hakan zai samu.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...