Lauyoyi sun yi zanga-zanga a Abuja saboda dakatar da Onnoghen

Protesters

Wadansu lauyoyi sun yi zanga-zanga kan dakatar da Babban Alkalin Najeriya Walter Onnoghen a gaban hedikwatar kungiyarsu (NBA) a Abuja ranar Litinin.

Masu zanga-zangar sun ce suna so ne Shugaba Muhammadu Buhari ya soke matakin dakatar da babban alkalin kasar.

A ranar Juma’a ne Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen bayan kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta umarce shi da ya yi hakan saboda tuhumarsa da kin bayyana kadakorinsa.

Har ilayau shugaban ya rantsar da Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin babban alkalin kasar.

Lauyoyin sun bukaci kungiyar NBA da ta fara yajin aiki kuma hukumar da ke kula da bangaren shari’ar da ta dakatar da sabon mukaddashin Alkalin Alkalin.

Yayin da suke zanga-zanga, an samu wani ayarin masu zanga-zanga da ya isa wurin, inda suke goyon bayan matakin Shugaba Buhari na dakatar da Onnoghen.

Hakkin mallakar hoto
PIUS UTOMI EKPEI

Image caption

An girke ‘yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA da ke Abuja ranar Litinin

A safiyar ranar Litinin, an girke ‘yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA, inda mambobin suka yi wani taron don tattauna batun dakatar da Alkalin Alkalin.

Kungiyar lauyoyin ta kira wani taron gaggawa a ranar Litinin, bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen.

Daya daga cikin lauyoyin da suka shiga zanga-zangar, sun ce Shugaba Buhari bai bi ka’ida ba wajen dakatar da alkalin.

Ya ce gwamnati ta nuna son kai don ya kamata ne kafin shugaban ya dauki matakin sai ya rubuta wa majalisar dattawan kasar.

Image caption

Hedkwatar NBA a Abuja

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...