Kwankwaso ya ce za su ci gaba da yakin neman zabe

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Hakkin mallakar hoto
Premium Times Nigeria

Bayan hukumar zaben Najeriya, INEC, ta dage zaben shugaban kasa wanda ta yi niyyar yi ranar 16 ga watan Fabrairun 2019, wata dambarwa da ta kunno kai ita ce ta batun ci gaba da yakin neman zabe.

A cikin wani jawabi da ya yi, shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce jam’iyyu ba za su ci gaba da yakin neman zabe ba a sauran kwanakin da suka rage kafin sabuwar ranar da aka ware domin yin zaben.

Lamarin da shugaban jam’iyyar APC Adam Oshimhole, ya ce ba za ta sabu ba a lokacin wata hira da manema labarai.

Adams Oshiomhole, ya ce a ka’idar doka shi ne, ana daina yakin neman zabe ne idan ya rage saura sa’oi 24 a yi zabe.

Don haka ya ce, kowa ya san wannan doka, sannna kuma jam’iyyarsu ta APC za ta ci gaba da yakin neman zabe tun da an dage sai wani makon.

Ya ce ‘ Zamu ci gaba da yakin neman zabe saboda mu nuna wa magoya bayanmu cewa kada su yi fushi abin da ya faru ya riga ya faru, don haka su fito su zabi dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyarmu ta APC a ranar zabe’.

A wani bangare kuma, shi ma mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wato sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba wani ne ya ce a daga zabe ba, to tunda an daga, sai su kyale kowa ya je ya fadi abin da zai fada a yakin neman zabe.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, Kwankwaso ya ce, sanin kowa ne ka’idar dokar hana zabe ita ce sa’oi 24 kafin zabe, to tun da an daga daga na zuwa mako guda da aka kara sai kowa ya je ya ci gaba da yakin neman zabensa.

Ya ce, dama abin da ake gudu ne ya faru.

Sanata Kwankwaso, ya ce ya tabbata ba bu wnada yaji dadin dage zaben nan, fatansa shi ne Allah ya sa kada a sake cewa an daga idan lokacin da aka sanya yazo.


Waiwaye

A ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a kasar.

Tun kafin karatowar zabe a kasar, hukumar zaben daidai da rana daya bata taba nuna cewa akwai matsala ko kuma tana fuskantar cikas ko tasgaro wajen samar da kayyayakin zaben ba.

Kwatsam sa’o’i kalilan kafin zaben, sai hukumar ta bayyana gazawarta a fili inda ta ce ba za ta samu damar gudanar da zaben ba saboda wasu matsaloli da suka sha karfinta.

Tun bayan haka, an ta yi samun ce-ce-kuce daga jama’a da jam’iyyun siyasa da ‘yan kasashen ketare dangane da wannan batu.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...